Tsaro: Shin Arewacin Najeriya Da Masu Mulki Sun Gaza


Fitaccen mai fafutukar kwato yancin al’ummar Najeriya kuma shugaban kwamitin Amintattun gamayyar kungiyoyin Arewa masu zaman kansu Alhaji Nastura Ashir Sherif ya bayyana sakamakon gazawar da masu mulki suka yi a halin yanzu na su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu wajen kare lafiya da dukiyar jama’a kamar dai yadda yake a cikin kundin tsarin mulkin kasa ya sa a halin yanzu za su tara dukkan al’umma domin kowa ya bayar da gudunmawarsa kan hanyar da za a bi wajen lalubo bakin zaren,saboda haka ne muke kokarin tabbatarwa da duniya cewa ba mu gaza ba a yankin Arewa.

Nastura Ashir Sherif ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da manema labarai, inda ya ce sun shirya yin wannan taro ne domin tattauna hanyoyin warware matsalar tsaron da arewacin Najeriya ke fuskanta tun da masu mulki a yanzu kowa ya san sun gaza ana kashe mutane a kullum kwanan duniya babu kakkautawa.

Ya ce za a yi taron ne a ranakun 20 da 21 ga wannan watan a garin Abuja hedikwatar tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Dattijo Farfesa Ango Abdullahi.

Ashir Sherif ya ci gaba da cewa “ta yaya mutanen da aka zaba domin kare mutunci, lafiya da dukiyar al’umma za su zauna al’amura na tafiya cikin halin da ake ciki a ko’ina na rashin tabbas?”.

“Kuma kamar yadda kowa ya Sani harkar tsaro kara tabarbarewa take yi, har yanzu ta kai ga a yankin Arewa maso Gabas yan Boko haram sun kai ga samun babbar Bindiga mai harbo jirgin sama ko duk wani abin da yake can nesa, wato bindigar da ake kira mai makaman roka, don haka dole ne mu tara jama’a domin kowa ya bayar da tasa gudunmawar a kan yadda za a warware wannan matsalar tsaron kafin ta hadiye dukkan jama’a musamman na yankin Arewa.

” mun kira yan kungiyoyi daban daban da suka hada da na dalibai, yan banga, yan kasuwa,direbobi, kungiyoyin ma’aikata da suka hada da na ma’aikatan asibiti da dukkan kowace irin kungiya domin kowa ya bayar da ta sa gudinmawa kan yadda za a samo bakin tsaren warware matsalar”.

Ya kara jaddada cewa ” Da aka dauke layukan wayoyin sadarwa a wasu kananan hukumomi cikin wasu Jihohi mun dauka za a kaiwa wadannan mutane yan bindiga ne farmaki ayi kaca kaca da su har cikin gidajensu amma sai muka ga sabanin hakan, ga lamarin na ta kara samun ci gaba a ko’ina cikin arewacin Najeriya, har ta kai ga mutane na tafiya cikin mota a tare su a kone su da motar baki daya mutane su Kone kurmus ta yadda ba mai iya gane su to, yaya zamu bari wannan ya ci gaba da faruwa?”. Inji Shugaban gamayyar kungiyoyi masu zaman kansu na Arewa.

Sai dai ya ce ba za su kira mutanen da a can baya suka kasa tsinana komai ba game da lamarin tsaro suk da irin gayyatar da suka rika yi masu a duk lokacin da za su yi wani taro ko kuma su irin wadancan mutanen suka gayyace su domin bayar da shawarwari kan yadda za a bullowa duk wata matsalar da ake saran nemo hanyoyin lalubo bakin tsaren

“Ya kamata jama’a su rika tunawa da irin mutanen da aka kashe a Gwaronyo a lokaci guda da kuma irin yadda mutane suka kasa bin hanyar garin Shinkafi zuwa koda babban birnin Jihar Zamfara ne da sauran abin da ke faruwa a sauran yankunan arewacin Najeriya na tsananin rashin tsaron lafiya da dukiyar jama’a wanda hakan ne ya sa muka tashi tsaye domin tattauna lamarin karkashin Dattijo Farfesa Ango Abdullahi”, inji Nastura Ashir Sherif.