Gwamnonin Arewa na mana karfa-karfa ta hanyar hanamu fadin abinda ke faruwa

Gwamnonin Arewa na mana karfa-karfa ta hanyar hanamu fadin abinda ke faruwa

Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Nijeriya “Coalition of Northern Groups” ta yi zargin cewa gwamnatocin arewacin kasar na rufe musu baki muddin suka nemi daukar fansa kan abin suka kira cin kashin da ake yi wa ‘yan arewa a kudancin kasar.

Abdul’aziz Sulaiman mai magana da yawun gamayyar kungiyoyin arewacin Nijeriya ya sanar da hakan ga DCL Hausa.

Yace bayanan da suke samu, ba su da dadin ji, ganin irin yadda ake dora wa wasu jinsin mutane laifi, domin laifin da wasu tsiraru daga cikinsu sun aikata.

Abdul’aziz yace bai kamata mutane su rika yanke hukunci da kansu ba, tare da sanin hakikanin abin da ya faru ba. Yace akwai bukatar mutane su hankalta, kowa nasa yake so.

Mai magana da yawun kungiyar, ya yi zargin cewa gwamnatocin arewa suna yi wa lamarin ‘yan yankinsu rikon sakainar kashi, ganin irin cin kashin da ake yi wa ‘yan Arewa Amma, ba a cewa uffan.

CNG News